in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da yara miliyan 1.6 a Najeriya na fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki
2016-07-21 10:01:49 cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), ya bayyana cewa, sama da yara miliyan 1.6 a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ne suke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Kwararriyar a sashen abinci mai gina jiki ta asusun na UNICEF, Florence Oni ce ta bayyana hakan a garin Kaduna a lokacin da take gabatar da rahoto a yayin wani taron bita na kwanaki na biyu na shekarar 2016 dangane da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na samar da abinci mai gina jiki cikin watanni shida da suka gabata a jihar, taron da aka saba gudanarwa bayan watanni shida-shida.

Jami'ar ta shaidawa mahalarta taron cewa, sama da yara 900,000 kwatankwacin kashi 57 cikin 100 na yaran da ke jihar sun tsunbure, wato yara 6 cikin kowa ne yara 10 'yan kasa da shekaru 5 da ke jihar ba sa girma saboda rashin abinci mai gina jiki.

A cewarta, tuni gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace don ganin an ceto wadannan yara daga mawuyacin halin da suke ciki.

Ta kuma kara da cewa, a watan Maris na wannan shekara, asusun na UNICEF tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kaduna, sun bullo da wani shiri na fitar da al'umma daga matsalar abinci mai gina jiki (CMAM), a wani bangaren na kokarin da ake yi na ganin an magance wannan matsala. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China