A wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan, ta bayyana rashin jin dadi game da barkewar rikicin tsakanin sojoji a makwaciyarta Sudan ta kudu, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa, kuma lamarin ya haifar da barazanar tsaro da rashin kwanciyar hankali.
Sanarwar ta kara da cewar, bisa irin damuwar da Sudan ke da shi game da zaman lafiyar Sudan ta kudun, shugaban kasar Sudan ya yi kira ga takwaransa Salva Kiir na Sudan ta kudu da mataimakinsa Riek Machar ta wayar tarho, inda ya bukace su da su ajiye son zuciyarsu, kuma su lalibo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Bugu da kari, ma'aikatar harkokin wajen ta ce tana cigaba da tuntubar kasashen duniya masu shiga tsakani, domin aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla na wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudun.
Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour zai halarci taron gaggawa na ministocin kasashen waje da za'a gudanar a Nairobin kasar Kenya a Litinin, domin tattauna batun.
A ranar Alhamis ne dai rikicin ya kaure tsakanin dakarun dake biyayya ga shugaban kasar Sudan ta kudun Kiir dana mataimakinsa Machar, a kusa da ofishin shugaban kasar dake Juba, daga bisani rikicin ya fantsama zuwa wasu sassan birnin.(Ahmad Fagam)