Jami'in bada jin kan Eugene Owusu, wanda ya kai ziyarar wuni guda yankin na Wau a ranar Alhamis, ya bayyana damuwa game da irin hasarar rayuka da ake samu a yankin, baya ga fararen hula da rikicin ya tilastawa barin gidadjen su da kuma wadanda suka fada cikin mawuyacin hali sakamakon rikicin.
Owusu ya fada a Juba cewa, wannan ba abu ne da za'a lamunce da shi ba. A cewarsa dole ne jami'an tsaro su tashi tsaye don sauke nauyin dake wuyansu na kare rayukan fararen hula da dakatar da duk wasu nau'oin hare hare a yankin.
Jami'in ya nuna damuwa matuka game da barkewar fadan tun daga ranar 24 ga watan Yuni, lamarin da ya haddasa mutuwar sama da mutane 40, sannan ya tilastawa a kalla mutane 70,000 barin gidajensu.
Bugu da kari kimanin mutane 12,000 ne ke neman mafaka a kusa da ofishin MDD dake jamhuriyar Sudan ta kudu wanda ke yankin na Wau.(Ahmad Fagam)