Deng ya ce akwai kwararan shedu dake tabbatar da cewar kaso 44 na yankunan Sudan ta kudun na da ma'adanan makare a karkashin kasa musamman zinare da tama da sauran ma'adanai masu daraja.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan ma'adanai na kasar Sudan Ahmed Muhammad Sadiq Al-Kanuri a birnin Khartoum.
Deng ya ce ya ziyarci Sudan ne domin samun muhimman bayanai game da yanayin taswirar Sudan ta kudu wadda a baya yanki ne daga kasar Sudan wanda ya balle a shekarar 2011.
A nasa jawabin ministan ma'adanai na Sudan ya shedawa 'yan jaridu cewar a shirye yake ya ba da muhimman bayanan da suka dace ga Sudan ta kudun. (Ahmad Fagam)