'Yan tawayen Al-shabaab na kasar Somaliya sun kai hari ga wani otel dake cibiyar birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya a jiya Asabar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11, a yayin da wasu mutane da dama suka jikkata. A halin yanzu, sojojin kasar sun kwace otel din daga hannun 'yan tawayen.(Lami)