A ranar Alhamis ne fada ya rincabe a garin Kidal, wani gari a yankin Hamada a arewacin Mali, tsakanin dakarun dake goyon bayan gwamnati, da 'yan tawayen Tuareg wadanda ke karkashin jagorancin Azawad Movements wato (CMA).
A wata sanarwa daga mai magana da yawun MDD ya ce, Ban, ya bayyana barkewar wannan fada a matsayin saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla a watan Yunin shekarar 2015, kana ya bukaci shugabannin bangarorin biyu da su dauki matakan da za su tabbatar da maido da zaman lafiya a kasar. (Ahmad)