in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Burundi ta sanar da niyyarta na halartar shawarwarin Arusha
2016-05-19 09:24:30 cri
Gwamnatin kasar Burundi ta bayyana niyyarta a ranar Laraba cewa za ta halarci shawarwari tare da bangaren adawar kasar dake ketare, da za a shirya a ranar 21 ga watan Mayu a birnin Arusha na kasar Tanzaniya a karkashin jagorancin masu neman daidaita rikicin Burundi. Mista Willy Nyamitwe, babban mai kula da harkokin sadarwa na fadar shugaban kasar Burundi, dake tsokaci a gidan rediyo mai zaman kansa na Isanganiro, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Burundi na daukar wadannan shawarwari a matsayin wani aikin ci gaban tattaunawa na tsakanin 'yan kasar Burundi na cikin gida. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China