in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kishirwa ta kashe mutane 34 a hamadar Nijar
2016-06-16 20:14:31 cri
Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa, an gano gawawwakin mutane 34 a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani sakamakon yunwa da kishirwa a cikin Hamada.

Shugaban yankin Arlit da ke arewacin kasar Nijar Alat Moutgaskia shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho. Yana mai cewa, 'yan ci-rani da suka gamu da ajalinsu wani bangare ne na tawagar 'yan ci ranin da suka yi nasarar tsallake shingen jami'an tsaro a kan hanyarsu ta zuwa kasar Algeria.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China