Zuma ya ce nasarorin da taron ya cimma sun dace da manufofin ci gaban nahiyar Afirka. Kaza lika ya bayyana matakai 10 da Sin ta gabatar a matsayin shaida, wadanda ke nuna kulawar da Sin ke yi da bukatun nahiyar Afirka, maimakon maida hankali ga bukatun kashin kai.
Ya ce da wadannan matakai 10 za a kai ga cimma manyan nasarori, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, da inganta samar da makamashi, da sauran fannoni da a baya ke fuskantar koma baya.
A bangaren nahiyar Afirka kuwa, shugaba Zuma ya ce kasashen nahiyar za su zage zamtse wajen cin gajiya daga alakar su da kasar Sin. Ya ce kasashen Afirka sun riga sun fara daukar matakai a wannan fanni, kuma Sin na ci gaba da tallafawa wajen warware wasu daga manyan kalubalen da nahiyar ke fuskanta.(Saminu)