in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ta Kudu ya tattauna kan rikicin da kasar ke fama da shi tare da takwaransa na kasar Uganda
2016-07-25 10:23:41 cri

Wani jami'in kasar Uganda ya bayyana a ranar Asabar da ta gabata, cewar a wannan rana ne shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya tafi kasar Uganda domin ganawa da shugaban kasar Yoweri Museveni, don tattaunawa game da rikicin Sudan ta Kudu.

Zaunannen sakataren ma'aikatar harkokin waje na kasar Uganda James Mugume ya fadawa manema labaru cewa, Yoweri Museveni ya gana da Salva Kiir a wannan rana a fadar shugaban kasar, inda suka tattauna kan yanayin tsaro na kasar Sudan ta Kudu, da kuma batun tura sojojin kasashen kungiyar IGAD zuwa kasar Sudan ta Kudu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashen kungiyar IGAD sun bayyana a gun taron shugabannin karo na 27 na kungiyar AU da aka yi a birnin Kigali, babban birnin kasar Ruwanda cewa, watakila za su tura sojoji zuwa kasar Sudan ta Kudu domin kaucewa tsanantar tarzoma a kasar. Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta bayyana a ranar 22 ga wata cewa, tana adawa da tura sojojin kungiyar IGAD zuwa kasarta. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China