in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayoyin manema labaru kan batun kasar Sudan ta Kudu
2016-07-20 16:17:11 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Laraba cewa, duk da cewar bangarori biyu na kasar Sudan ta Kudu dake tada rikici sun sanar da tsagaita bude wuta, amma har yanzu kasar tana cikin halin kiki-kaka na rashin tabbatacciyar makoma. Kasar tana bukatar taimakon kasashen duniya domin kyautata mummunan halin da jama'a suke ciki a kasar.

Mr. Lu ya kara da cewa, kasar Sin tana kokarin tabbatar da yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. Bayan da aka samu sauyawar yanayin al'amaru a kasar Sudan ta Kudu, kasar Sin ta tuntubi bangarori daban daban da batun ya shafa ta hanyar shiga tsakani, domin ingiza shawarwari cikin lumana, ta yadda bangarori biyu na kasar Sudan ta Kudu za su tsagaita bude wuta tare da hanzarta yin shawarwari .

Bugu da kari, Lu Kang ya bayyana cewa, yau ne jakada Zhong Jianhua, wakilin musamman mai kula da harkokin Afrika na kasar Sin ya kai ziyara a kasashen Habasha da Uganda da Kenya da sauran kasashen da batun kasar Sudan ta Kudu ya shafa, inda bangarori daban daban za su yi musayar ra'ayi game da gudanar da aikin shiga tsakani kan yadda za a nuna goyon baya ga kungiyar IGAD, a kokarin da ta ke yi na ganin an gaggauta shimfida zaman lafiya a kasar da kuma kalubalantar bangarori biyu na kasar da su tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da aka cimma a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China