in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta bukaci Masar da kasashen Larabawa da su yi watsi da kiran kasashen waje na neman shiga tsakani
2016-07-18 10:13:06 cri

Jakadan kasar Sudan ta kudu da ke birnin Alkahiran Masar Anthony Kon ya bukaci kasar Masar da kungiyar kasashen Larabawa, da su yi watsi da duk wani tayin shiga tsakanin na sojojin kasashen ketare a fadan da ke faruwa yanzu haka a kasarsa.

Jakada Kon wanda ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai a birnin Alkahira, ya kuma tunatar da kasar Masar game da gwagwarmayar da suka yi ta kin jinin mamayer da Burtnaiya ta yiwa kasashen nasu. A saboda haka, kamata ya yi Masar ta yi watsi da duk wani tayi na tura sojojin MDD zuwa Sudan ta kudu.

Jakadan ya ce duk wani kokarin shiga tsakanin da sojojin ketaren za su yi a fadan da dakarun sassan biyu ke gwabzawa a kasar, yana iya shafar harkokin tsaron kasashen Larabawa, da ma kasar ta Masar.

A kwanakin nan ne dai fada ya barke a birnin Juba tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da na mataimakin shugaban kasar Riek Machar, inda aka kashe mutane da dama.

A watan Agustan shekarar da ta gabata ce dai Kiir da Machar suka rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kai ga kafa gwamnatin hadaka ta wucin gadi da nufin kawo karshen yakin basasar kasar na sama da shekaru biyu. A watan Afrilu ne kuma aka kafa gwamnatin hadaka wadda za ta jagoranci kasar kafin a shirya zabuka cikin watanni 36.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China