Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin watsa labarai da dab'i da rediyo, telebijin da fina-finai ta majalisar gudanarwar kasar Sin Tong Gang ya bayyana a gun bikin rufe taron cewa, an shirya taron ne yayin da aka cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, yawan mahalarta taron ya zarce yawan wadanda suka halarci tarukan da aka gudanar a baya, kana an samu babban sakamako a gun taron.
Rahotanni na cewa, yarjejeniyoyi 15 da sassa biyu suka sanyawa hannu sun hada da takardar fahimtar juna ta hadin gwiwar hukumar kula da harkokin watsa labaru da dab'i da rediyo da telebijin da fina-finai ta kasar Sin da hukumar watsa labaru ta kasar Zimbabwe, iznin watsa shirye-shirye 4 a kasashen Mauritania, Uganda, Nijer da Togo da dai sauransu.
A cikin sanarwar hadin gwiwar, kasashen Afirka sun kuma nuna goyon baya ga Sin da kasashen da rikicin tekun kudancin Sin ya shafa da su warware matsalar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. (Zainab)