A yayin ganawar, mista Liu ya nuna tabbaci ga sakamakon da aka samu a taron, ya kuma yaba da hadaddiyar sanarwar da aka cimma. Liu ya kara da cewa, taron tattaunawar wani muhimmin sashe ne na hadin kan sada zumunci dake tsakanin Sin da kasashen Afika.
Ya ce, kasar Sin na fatan yin kokari tare da bangaren Afirka, don kara yin cudanya da hadin kai tsakanin kafofin watsa labarun bangarorin biyu, da karfafa hadin kai a tsakaninsu, ta yadda za a inganta bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka yadda ya kamata.
A nasu bangare, mista Moustapha Ali, ministan watsa labaru na kasar Chadi, kasar da ke shugabantar kungiyar AU a halin yanzu, da kuma sauran wakilan kasashen Afirka a wannan taro suna ganin cewa, hakika hadin kai tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da kasashen Afirka na iya tabbatar da samu moriyar juna da samu nasara tare, kuma yana da ma'ana sosai wajen kara matsayin bunkasuwar kafofin watsa labarun kasashen Afirka, da karfafa tasirin kasashe masu tasowa. (Bilkisu)