Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa, an kama Barry ne a ranar Talata a kusa da dajin Wagadou daf da kan iyakar kasar Mauritaniya.
An haifi mutumin da ake zargin ne a shekarar 1979, kuma na hannun daman Amadou Kouffa ne, shugaban kungiyar 'yan ta'adda ta MLF wadda ke aiki kafa da kada da Ansar Dine.(Ibrahim)