in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali ta sanar da ayyana dokar-ta-baci
2016-07-21 10:48:43 cri
A jiya Laraba ne shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya shugabanci taron majalisar ministocin kasar, inda aka tsaida kudurin ayyana dokar-ta-baci har na tsawon kwanaki 10 a kasar tun daga yau Alhamis 21ga wata.

Wata sanarwa da aka bayar ta bayyana cewa, an ayyana dokar bacin ce sakamakon barazanar ta'addanci da kasar Mali ke fuskanta. Haka kuma tun daga yau, an tsaida kudurin ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 3 a dukkan fadin kasar Mali don nuna juyayi ga sojojin da suka mutu a sakamakon harin da aka kai a sansanin soja dake tsakiyar kasar Mali a kwanakin baya.

A ranar 19 ga wata ne, wasu dakaru suka kai hari kan wani sansanin soja dake yankin Nampala na tsakiyar kasar Mali, wanda ya haddasa mutuwar sojoji 17 yayin da mutane 35 suka ji rauni. Bayan faruwar harin, wata kungiyar dakarun da ke kare muradun Fulani ta kasar Mali ta sanar da daukar alhakin kai harin ta wani gidan rediyo mai zaman kansa, daga baya kuma kungiyar Ansar Dine ita ma ta sanar da cewa, ita ce ta kai wannan hari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China