Mali: Sojoji guda biyu da aka bada sanarwar sun mutu a cikin wani harin sun dawo gida
Kaporal Zakaria Coulbaly da Adama Zongo sun sake bayyana a ranar Asabar a cikin gidajensu a Markala, dake kasar Mali, a yayin da kuma sunayensu suke cikin jerin sunayen sojojin da aka kashe a wani sansaninsu na Nampala a ranar 19 ga wata. Sojojin sun bayyana cewa, gaban nasasar da maharan suka samu kan rukuninsu, sun fidda tufafinsu na soja sun gudu zuwa a kasar Mauritaniya domin jiran zuwa taimakon sojoji a Nampala. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku