Bayan faruwar harin, shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya gudanar da taron majalisar tsaron kasar, inda aka tattauna halin tsaro da ake ciki a kasar. Bayan taron, Tall ya bayyana yawan sojojin da suka mutu da wadanda raunata a sakamakon harin, amma bai bayyana yawan mutanen da suka kai harin da kuma wadanda suka mutu ko suka ji rauni ba.
A wannan rana, kungiyar dakarun da ke kare muradun Fulani ta kasar Mali ta sanar da kai wannan hari. Bayanai na cewa,wannan kungiya dai sabuwa ce a kasar. (Zainab)