160602-WHO-bai-kamata-a-jinkirta-ko-soke-gudanar-da-gasar-wasannin-Olympics-ta-Rio-ba-domin-cutar-Zika-zainab.m4a
|
Akwai saura watanni biyu ko fiye da za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta Rio, amma yanzu cutar Zika tana yaduwa a kasar Brazil. Koda yake yawancin mutane masu kamu da cutar ta hanyar cizon sauro, amma za a iya yada cutar a tsakanin mutane ta hanyar jima'i. mutane masu kamu da cutar za su ji zazzabi kadan, ciwon fata, ciwon ido da sauransu har na tsawon kwanaki 2 zuwa 7. Amma wannan cuta ta kawo babbar illa ga masu sami ciki.
A cikin wasikar, masana sun bayyana cewa, yaduwar cutar Zika ta kawo babbar barazana, wadda za kawo hadarin kamu cutar ga masu yawon shakata dubu 500 daga wurare daban daban na duniya. Idan su kamu da cutar da koma kasashensu, musamman a kasashen da ba a samu cutar Zika ko maras samun cikakken sharadin likitanci, kamar nahiyar kudancin Asiya da nahiyar Afirka, watakila za a haifar da babbar matsala.
Wasikar ta yi kira ga hukumar WHO da ta sake yin sabbon bincike kan yanayin cutar Zika a kasar Brazil, da bada sabuwar shawara ga masu yawon shakatawa da za su zo kasar.
Game da wannan, hukumar WHO ta bayar da sanarwa a kwanakin baya cewa, gudanar da gasar wasannin Olympics ta Rio bisa shirin da aka yi ba zai canja yanayin yaduwar cutar Zika ba. Bisa binciken da aka yi, cutar Zika tana yaduwa a kasashe da yankuna kimanin 60 a duniya, ciki har da kasashe da yankuna 39 a nahiyar Amurka. Kasar Brazil tana daya daga cikinsu, amma mutane su kiyaye zo kasar domin dalilai iri daban daban. Hanya mafi kyau wajen rage hadarin kamu da cutar ita ce bin shawara game da yawon shakatawa, hukumar WHO za ta ci gaba da sa ido ga yanayin yaduwar cutar, da kuma gabatar da sabuwar shawara idan aka samu canji.
Hakazalika kuma, bisa binciken da aka yi a kwanakin baya, yanzu yaduwar cutar Zika ta fi tsananta a arewa maso gabashin kasar. Amma birnin Rio de Janairo tana zauna a kudu maso gabashin kasar. Kana an kashe sauro a yankunan da tawagogin 'yan wasa da masu yawon shakatawa, wannan aiki zai taimakawa magance yaduwar cutar Zika.
Haka kuma, hukumar WHO ta bada shawara ga 'yan wasa da masu yawon shakatawa da suka je birnin Rio da sauran yankuna masu fama da cutar Zika su bi shawarwarin yawon shakatawa da hukumar WHO da hukumomin kiwon lafiya suka gabatar, don magance kamu da cutar yayin da suke a kasar Brazil.
Bisa labarin da aka bayar a tashar internet ta gasar wasannin Olympics ta Rio, ministan kiwon lafiya na kasar Brazil Richardo Barros ya gana da jami'an kwamitin wasannin Olympics na duniya a birnin Geneva a kwanakin baya, inda ya bayyana cewa, za a kara nemi likitoci dubu 6 don tabbatar da kiwon lafiya yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Rio a bana, kana kwamitin wasannin Olympics na duniya sun yi imani ga wannan kuduri.
A makon da ya gabata, ministan kiwon lafiya na kasar Brazil ya gana da gwamnan jihar Rio da magajin gari na birnin Rio, inda suka tattauna matakan magance yaduwar cutar Zika da kiwon lafiya a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio. Kana yayin da yake ganawa da babban direktan kwamitin wasannin Olympics na duniya Christophe De Kepper da shugaban ofishin kula da kiwon lafiya Richard Budgett, Barros ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Brazil, da ta jihar, da ta birnin Rio za su hada kai don tinkarar matsalolin hana yaduwar cutar Zika, da rashin samun likitoci da sauransu.(Zainab)