in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha za ta goyi bayan sojojin saman gwamnatin Syria
2016-06-07 14:11:50 cri
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya bayyana a jiya Litinin cewa kasarsa, za ta goyi bayan sojojin saman gwamnatin kasar Syria cikin himma da kwazo.

Rahotanni na cewa bayan ganawar Mr. Lavrov da takwaransa na kasar Finland Timo Soini, Mr. Lavrov ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasarsa na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa da Amurka, a wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda dake kasar Syria, ko da yake Rasha na kaucewa jinkiri wajen aiwatar da hakan, don gudun kada 'yan adawa da gwamnatin Syria su samu lokaci na farfado da karfin su.

Kaza lika, ya ce, kasar Rasha ta taba yi wa Amurka gargadin kara tabarbarewar yanayin tashin hankali a yankin Aleppo, inda ta ce za ta samar da taimako ta sama ga sojojin gwamnatin Syria.

A wani ci gaban kuma, Mr. Lavrov ya ce yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka John Kerry har karo uku cikin makon da ya gabata, ya jaddada cewa kasarsa na adawa da dukkanin matakan da tsagin 'yan adawar Syria ya dauka bisa goyon bayan kasar Turkiya. Ya ce, ya kamata kasar Amurka ta cika alkawarinta na daukar matakai yadda ya kamata, wajen hana shigar dakaru da makamashi daga Turkiya zuwa Syria, har sai an kammala aikin rabe tsakanin dakarun 'yan adawa da gwamnati da kuma bangaren kungiyoyin ta'addanci na kasar ta Syria.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China