Rutskoy ya bayyana a gun taron manema labaru da ma'aikatar tsaron kasar ta gudanar a wannan rana cewa, an kyautata halin tsaro da ake ciki a kasar Syria, an kwantar da hankali a wuraren da aka dakatar da ayyukan soja. Amma kungiyar Al-Nusra tana yunkurin lalata yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da tsananta halin da ake ciki a wasu yankunan kasar Syria. Kana kuma kungiyar Al-Nusra ta yi amfani da yarjejeniyar don zama tare da kungiyar da ke adawa da gwamnati mai sassaucin ra'ayi ta kasar don magance harin sama da Rasha take kai mata.
Rutskoy ya kara da cewa, a halin yanzu, kungiyar ta'addanci ta samu isassun makamai, kuma ta mayar da karfin sojansu, kana sun fara kai hare-hare a birnin Aleppo da yankin Homs. A kwanakin baya, Rasha ta bada shawara ga kasar Amurka da su hada kai don kai hare-haren sama ga kungiyar mai tsattauran ra'ayi da ta ta'addanci a kasar Syria, amma Amurka ba ta amsa shawarar Rasha ba. A cewar Rutskoy, wannan zai haddasa tsanantar da halin da ake ciki a kasar. (Zainab)