Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a lokacin gabatar da tawagar 'yan wasan na Najeriya ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympic (NOC) jiya Talata a Abuja.
Ya ce wannan umarnin ya zama dole sakamakon irin fatan da gwamnatin kasar ke da shi wajen samun nasara a gasar wasannin ta Brazil.
Sai dai shugaban na Najeriya, ya gargadi 'yan wasan da su guji aikata duk wani abu da ka iya zubarwa kasar kima, kana ya hore su su zama jakadu na gari ga Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce baya ga cancantar 'yan wasan na shiga wasannin na Olympic, haka kuma, 'yan wasan na Najeriya, sun cancanci shiga gasar wasanni ta Paralympic.
Ita dai gasar wasannin ta Paralympic, za'a gudanar da ita ne da zarar an kammala gasar wasannin Olympic.
Sannan ya taya 'yan wasan murnar samun nasarar shiga gasar duk da irin kalubalen da suka fuskanta a yayin shirye shiryen shiga gasar, kana ya bukaci 'yan wasan da su kara kaimi don samun nasarar lashe lambar yabo ga kasar.
A jawabinsa ministan wasannin na Najeriya Solomon Dalong, ya baiwa shugaban kasa da al'ummar Najeriya tabbaci wajen samun nasarar a gasar. (Ahmad)