in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Rio zai bada kyautar tikitin kallon gasar Olympic 500,000
2016-06-01 17:48:08 cri
Masu shirya gasar wasannin Olympic na birnin Rio de Janeiro, sun ce za su bayar da kyautar tikiti 500,000, na kallon wasannin gasar da za a gudanar a birnin, ga yara da kuma ma'aikatan gwamnati.

Hukumar birnin ta ce tuni aka ware kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 14 domin wannan kuduri, kuma wadanda za su amfana daga wannan garabasa sun kunshi dalibai masu hazaka, da ma'aikata wadanda ke aikin tallafawa gajiyayyu, da kuma ma'aikatan gwamnati da suka bada gudummawa mai ma'ana ga ci gaban harkokin wasanni ta kafofin sada zumunta na zamani.

A cewar sakataren ofishin magajin garin birnin na Rio Pedro Paulo, manufar wannan mataki ta hada da inganta alakar al'ummar kasar Brazil da sha'anin wasanni musamman na nakasassu, tare da bunkasa aikin sayar da tikitin da ake gudanarwa.

Ya zuwa yanzu dai an sayar da kusan daya bisa uku na jimillar tikiti miliyan biyu da rabi na kallon wasan nakasassun wanda za a gudanar tsakanin ranekun 7 zuwa 18 ga watan Satumba. A bangaren gasar masu cikakkiyar lafiya wadda za a gudanar tsakanin ranekun 5 zuwa 21 ga watan Agusta, tuni aka sayar da tikiti miliyan 3 da rabi, cikin jimillar tikiti miliyan 5 da dubu dari biyar da aka tanada.

Game da tikitin da aka kebe domin rabarwa kyauta kuwa, ma'aikatan gwamnati za su samu tikiti 64,524, na kallon gasar nakasassu da kuma wasu tikitin 4,000 na ragowar wasannin da za a gudanar.

An ce ma'aikatan da suka gabatar da hotuna da bidiyo na sakwannin tallata wannan gasa dake tafe, na iya samun tikitin na kyauta. Kaza lika an warewa yara 'yan makaranta tikiti 177,000 na kallon gasar nakasassu, baya ga wasu karin tikitin 19,000 na gasar wadanda ba nakasassu ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China