Liu Jieyi ya bayyana a gun muhawarar kwamitin sulhun kan batun hanyoyin gudanar da ayyuka cewa, kamata ya yi membobin kwamitin sulhun su tattauna tare, a wani mataki na kokarin cimma daidaito, yayin da kwamitin sulhun da hukumomin da yake jagoranta ke tsaida kuduri.
Ya ce idan bangarori daban daban na da bambancin ra'ayoyi, ya kamata a magance hakan ta hanyar tsaida kuduri, da neman cimma daidaito, da kiyaye ikon kwamitin sulhun.
Haka zalika kuma, Liu Jieyi ya yi kira ga kwamitin sulhun da ya kara azama wajen aikin shiga-tsakani, da hadin gwiwa, don magance amfani da hanyoyin kawo barazana, ko saba takunkumi da dai sauransu. (Zainab)