Bayan da hukumar Standard & Poor's ta sanar da wannan kuduri, gwamnati da bangarorin tattalin arziki na kasar Afirka ta kudu dukkansu sun saki jikinsu. Darajar kudin Rand da take ta raguwa ta samu hauhawa fiye da kashi 3 cikin kashi dari a jiya.
Sannan, ma'aikatar kudi ta kasar Afirka ta kudu ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa tana maraba da kudurin hukumar Standard & Poor's. Bugu da kari, ma'aikatar ta ce, wannan kuduri zai sa kasar Afirka ta kudu da ta samu karin lokacin yin gyare-gyare domin cimma burin samun ci gaban tattalin arziki daga dukkan fannoni da kuma aiwatar da manufofin kebe kasafin kudi ga ayyukan more rayuwar jama'a ba tare da kasala ba. (Sanusi Chen)