in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tanzania ya sallami shugaban cibiyar yaki da cin hanci
2015-12-17 10:54:40 cri
A Jiya Laraba, sabon shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya sallami babban darektan cibiyar rigakafi da yaki da cin hanci na kasar, mista Edward Hoseah, dalilin rashin kwarewarsa.

Sakataren farko na gwamnati, mista Ombeni Sefue, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaba Magufuli bai gamsu da yadda cibiyar rigakafi da yaki da cin hanci (PCCB) take cika aikinta ba. Shugaban kasar ya bayyana rashin jin dadinsa ga cibiyar PCCB da kasa yin bincike a cikin tashar ruwan Dar es Salaam, lamarin da ya janyo asarar kudin shiga ga gwamnati ta hanyar ficewar kudin haraji, in ji mista Sefue. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China