in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta baiwa Tanzaniya dala milyan 11 don tallafawa yan gudun hijirar Burundi
2016-02-02 10:39:14 cri
MDD ta amince da sakin dala miliyan 11 ga kasar Tanzaniya domin bada taimakon gaggawa ga 'yan gudun hijira da rikici ya daidaita daga kasar Burundi.

Sama da 'yan kasar Burundin 126,000 ne suka tsallaka zuwa Tanzaniya tun a watan Aprilun shekarar 2015, a sakamakon rikicin siyasar da ya rincabe a kasar.

Da ma dai akwai 'yan gudun hijirar kimanin 64,000 daga jamhuriyar Congo dake neman mafaka a kasar tuntuni, a yanzu haka, kasar Tanzaniya tana da 'yan gudun hijira sama da 193,000.

A kowace rana, an kiyasta kusan mutane 1,500 ne ke kwarara kasar, bisa ga hasashen da aka yi, ana saran kasar zata karbi bakuncin yan gudun hijira da zasu kai 230,000 nan da karshen wannan shekarar.

Babban sakataren MDD Ban Ki moon ya fada cerwar akwai babban kalubale na samar da kayayyakin tallafi da kuma bada kariya ga 'yan gudun hijirar.

Sanarwar ta kara da cewar gudummawar MDD, zata taimaka wajen samar da kayayyakin jinkai ga 'yan gudun hijirar Burundi wadanda ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira dake yankunan Nyarugusu, da Nduta da kuma Mtendeli a shiyyar Kigoma da ke yammacin kasar ta Tanzania.

Sanarwar ta ci gaba da cewa za'ayi amfani da kudaden wajen samarwa alummonin dake gudun hijirar ruwa mai tsabta da muhalli mai tsabta da kiwon lafiya da kuma abinci da wuraren zama.

Sannan wani kaso daga cikin kudaden za'ayi amfani dasu wajen shawo kan cutar gudawa data barke, harma ta shafi mutane a kalla 19. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China