Mataimakin mai magana da yawun majalisar Ben Bruce, ya shedewa 'yan jaridu jim kadan bayan kammala taron sirri na tsawon sa'o'i biyu da ya gudana tsakanin sanatoci da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.
Bruce ya ce bayanin da Emefiele ya yi a zauren majalisar ya yi daidai da sashe na 8 na dokokin bankin CBN na shekarar 2007, wanda ya bukaci gwamnan ya dinga bayyanawa majalisar halin da ake cikin game da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki lokaci zuwa lokaci.
Ya ce gwamnan na CBN, ya ba da cikakken bayani game da irin halin da tattalin arzikin kasar ya tsinci kansa cikin shekarar da ta gabata.
Bruce ya ce, jawabin na Emefiele ya fara ne da bayyana yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, musamman batun faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
A cewarsa, Emefiele ya bayyana karara game da kalubalen da kasar ke fuskanta sakamakon gibin kashi 70 cikin 100 da kasar ta samu na gangar danyen mai wanda ake sayar da shi a kana dala 116 a watan Yunin 2014, inda ya koma dala 30 kan kowace ganga a farkon shekarar 2016.
A ranar 25 ga watan Mayu, majalisar ta bukaci gwamnan CBN da ministar kudi da su bayyana a zauren majalisar, domin yin karin haske game da sha'anin kudi da yanayin tattalin arzikin kasar. (Ahmad)