An kuma bayar da wata sanarwar hadin gwiwa bayan kammala ganawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwarorinsa daga kasashe 10 mambobin kungiyar ASEAN da ya gudana a babban birnin kasar Laos a lokacin taron ministocin harkokin wajen kungiyar ta ASEAN karo na 49.
Kasashen sun bayyana cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin, shi ne babban muradun kasashe mambobin kungiyar da Sin har ma da duniya baki daya.(Ibrahim)