A cikin wannan sanarwa, an ce MDD ta dora muhimmanci sosai kan tattaunawar da ake yi a wannan karo, inda Hervé Ladsous, mataimakin babban magatakardan Majalisar mai kula da aikin wanzar da zaman lafiya, da Atul Khare, mataimakin babban sakatare mai kula da aikin samar da abinci da kayayyaki ga sojojin wanzar da zaman lafiya, dukkansu sun gana da tawagar jami'an kasar Sin daya bayan daya.
Jami'an biyu na MDD sun nuna juyayi kan rasa ran wani sojan kasar Sin a kasar Mali, kuma sun nuna jaje ga sojojin Sinawa wadanda suka ji raunuka sakamakon harin da aka kai musu. Haka zalika sun kuma nuna yabo kan gudunmawar da kasar Sin take bayar wa ga aikin wanzar da zaman lafiya a kasashe daban daban.(Bello Wang)