Sanarwar ta ce, an tabbatar da cewa, ma'aikata guda biyu wadanda aka sanar da rasuwarsu a kwanan baya, sun ji raunuka masu tsanani, amma ba su rasu ba. Yanzu, ana yi wa wadannan ma'aikata 'yan kasar Mali jinya a asibitin Gao. Sabo da haka, adadin karshe na yawan ma'aikatan tawagar MINUSMA da suka rasu sakamakon wadannan hare-hare biyu ya kai guda biyu, tare da wasu ma'aikata hudu suka ji raunuka masu tsanani, sauran ma'aikata 11 sun samu raunuka marasa tsanani. Daga cikinsu, sansanin da sojojin kasar Sin masu wanzar da zaman lafiya a kasar Mali ke zaune ya samu asara mafi tsanani, inda wani sojan kasar Sin ya rasu, tare da wasu sojoji biyar da suka jikkata, daga cikinsu biyu na cikin mawuyacin hali mai tsanani sosai.
A ran 1 ga watan Yuni, kungiyar Al-Qaida ta Islamic dake yankin Maghreb ta sanar da daukar alhakin kai wadannan hare-hare biyu. (Sanusi Chen)