Rahoton ya nuna cewa, bisa shirin yaki da cutar Sida mai amfani a wasu yankuna, an ce za a samu gagarumin ci gaba wajen shawo kan cutar nan da shekara ta 2030. Ana sa ran zuwa waccan lokacin, za a samu raguwar adadin mutanen da suke mutuwa sakamakon cutar da aka kiyasta zai kai miliyan 21, kuma za a rage yawan mutanen da suke kamuwa da cutar da miliyan 28. Don kawo karshen wannan cutar da ta kawo kalubale sosai game da lafiyar jikin dan Adam, ya kamata a gaggauta daukar wasu matakai, wato a yi amfani da lissafi, don jan kunnen mutane, wadanda za su fi saurin kamuwa da cutar, kamar yadda aka fada a cikin rahoton.(Bako)