in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton MDD: An hana yaduwar cutar sida a duk fadin duniya
2015-07-15 10:15:26 cri

Hukumar yaki da cutar AIDS ta MDD wato UNAIDS ta bayar da wani rahoto jiya Talata, cewar kawo yanzu an kai ga cimma burin tsayar da kuma hana yaduwar cutar sida a duk fadin duniya, kamar yadda ya ke kunshe cikin shirin muradun karni na MDGs. Haka zakila, ana sa ran cimma burin kawo karshen yaduwar cutar ya zuwa shekarar 2030.

A cikin wannan rahoto mai lakabin "Yadda cutar sida ta canja al'amura", an nuna cewa, tun baya da aka gabatar da matakan shawo kan cutar cikin shirin muradun karni na MDGs a shekarar 2000, ya zuwa yanzu an rage adadin yawan mutane miliyan 30 da ke da hadarin kamuwa da kwayar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki, baya ga rage mutane miliyan 8 da ake fargabar za su mutu sakamakon cutar.

A nasa bangare, Michel Sidibe, daraktan hukumar UNAIDS ya yi tsokaci cewa, ana kara samun yawan jarin da ake sakawa kan batun tinkarar cutar kanjamau. Don haka, idan har hakan ya dore, babu makawa za a iya kawo karshen yaduwar cutar ya zuwa shekarar 2030.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China