A yammacin ranar 8 ga wata firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da babban sakataren MDD Ban Ki-moon dake ziyara a kasar Sin.
A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin ta yi kokarin tabbatar da tsarin duniya dake bisa tushen tsarin MDD, da kiyaye manufofin tsarin mulkin MDD, da sa kaimi ga warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, da shiga hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa kan manyan kalubale ciki har da tinkarar sauyin yanayi, da kuma samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.
Li Keqiang ya yabawa Ban Ki-moon kan gudummawarsa wajen sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da MDD, ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan MDD da tabbatar da ikon MDD, kuma tana son yin kokari tare da bangarori daban daban wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da wadata a duniya.
A nasa bangare, Ban Ki-moon ya jajantawa Sin game da bala'in ambaliyar ruwa da aka samu a kudancin kasar, ya yi imani cewa, jama'ar kasar Sin za su cimma nasarar yaki da bala'in a karkashin jagorancin gwamnatin kasarsu. Kana MDD ta yabawa kasar Sin game da gudummawar da take bayar wajen yaki da bala'u da samun bunkasuwa mai dorewa a duniya, kuma tana fatan Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen cimma ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030 da tinkarar sauyin yanayi da sauransu. (Zainab)