in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kara wa juna sani kan sassaucin ra'ayin addinin Musulunci a Urumqi
2016-07-21 10:54:15 cri

A jiya Laraba ne, aka shirya wani taron kara wa juna sani na kasa da kasa game da sassaucin ra'ayi a addinin Musulunci, taron da ya gudana a birnin Urumqi na jihar Xinjiang na Ugyur mai cin gashin kanta da ke nan kasar Sin.

Malaman addininin Musulunci, da kwararru da jami'an gwamnati kusan dari 1 wadanda suka fito daga kasashen Sin da Rasha da Khazakstan, da Tajikstan da Kirkistan da Uzebikstan ne suka halarci taron.

Babban jigon wannan taro shi ne "Amfani da akida mai sassauci maimakon tsattsauran ra'ayi". Mahalarta taron suna ganin cewa, ta'addanci da ayyukan nuna karfin tuwo da su kan faru, sun zama wata babbar matsala ga kokarin tabbatar da zaman lafiya a shiyya-shiyya, har ma a duk fadin duniya, baya ga zama kalubale ga daukacin bil Adama. Masu tsattsauran ra'ayi su kan yi amfani da wasu tunanin da suka sabawa dokokin addini domin canja tunanin jama'a. A don haka ya kamata musulmai su tashi tsaye su hada kai wajen yada sassaucin akida a kokarin karfafa yin mu'amala da koyi da juna da sauran kabilu da addinai da al'adu domin kokarin tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya da samun jituwar al'ummomi.

Chen Guangyuan, babban limani, kuma shugaban kungiyar Musulmai ta kasar Sin ya bayyana cewa, Alkur'ani mai tsarki ya yi horo da bin sassaucin akida maimakon tsattsauran akida, kuma umarni ne da ya kasance wabiji ga musulmai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China