in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada aniyar kula da al'amurran addini
2016-04-24 13:52:33 cri

An yi taron inganta al'amurran addini a kasar Sin daga ranar 22 zuwa ranar 23 ga wata a nan birnin Beijing.

Babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi inda ya bayyana cewa, batun addini na da muhimmanci sosai, dole ne jam'iyyyar kwaminis ta Sin ta daidaita shi yadda ya kamata, kana batun addini na da muhimmin matsayi daga cikin dukkan ayyukan jam'iyya da gwamnatin kasar ke aiwatarwa.

A halin yanzu, kasar Sin na gudanar da ayyukan addini yadda ya kamata.

Bugu da kari, Xi Jinping ya nanata cewa, dole ne a bi manufar da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta tsara domin gudanar da ayyukan addini da kyau. Ya kamata a tabbatar da 'yancin jama'a na bin addinai da kula da harkokin addini bisa doka, domin cimma daidaito a tsakanin harkokin addinai da na zaman al'umma na gurguzu. Kuma ya kamata a kara yin bincike kan harkokin addini a dukkan fannoni domin daidaita su yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China