in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata Amurka ta tsoma baki kan harkokin addini na sauran kasashe ba
2016-05-05 20:15:31 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce ya kamata kasar Amurka ta dubi kanta kan harkokin addini, bai kuma dace ta rika tsoma baki kan harkokin addini na sauran kasashe ba.

Mr. Hong ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a Alhamis din nan lokacin da yake amsa wata tambaya. Ya ce a kwanakin baya, hukumar kula da harkokin addini ta kasar Amurka ta gabatar da rahoton ta na bana, inda ta ci gaba da maida kasar Sin a matsayin kasar da rahoton ya fi maida kai kan ta.

Game da wannan batu Hong Lei ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na girmama, da tabbatar da 'yancin bin addinai, kuma jama'ar kasar Sin tana da ikon bin addini da take so cikin 'yanci. Sai dai a cewar sa kasar Amurka ta kyale batu na gaskiya, tana kuma fidda rahoto game da wannan fanni na shekara shekara, wanda ke zargi manufofin addini na Sin da halin kasar ke ciki a wannan fanni.

Mr. Hong Lei ya kara da cewa kasar Sin ba za ta amince da wannan rahoto ba, za kuma ta ci gaba da tuntubar Amurka domin kamo bakin zaren wannan batu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China