in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin jin dadin ta a game da hana 'yancin addini da Amurka tace tana yi
2015-05-04 20:26:47 cri
Kasar Sin ta mika koken ta na rashin jin dadi akan yadda kwamitin bada shawara na kasa na Amurka ta saka sunan ta cikin kasashen da ake da damuwa na musamman game da hidimar addini.

Wannan korafin ya zo ne bayan da kwamitin na gwamnatin Amurka a kan harkokin 'yancin yin addini na kasa da kasa ta bayyana rahoton ta na shekara shekara a ranar alhamis din da ta gabata cewar kasar Sin tana cikin kasashen da ake da damuwa matuka akai, kuma sauran jerin kasashen sun hada da Vietnam, Myanmar da Korea ta arewa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce rahoton na dauke da banbancin siyasa da kuma zargi wadanda basu da tushe bare makama wanda kasar bata amince da shi ba ko kadan.

A ganawarta da manema labarai a litinin din nan Madam Hua tace gwamnatin kasar Sin tana mutunta tare da kare cikakken 'yancin addinin jama'ar ta.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China