Shugaban rundunar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali wato MINUSMA Mahamat Saleh Annadif, ya ziyarci birnin Gao da ke arewacin kasar ta Mali a jiya Alhamis, inda ya gabatar da jaje ga sojojin MDDr da aka kaiwa harin ta'addanci a ranar 31 ga watan Mayun da ya shude. Ya kuma sake nanata aniyar MDD ta ci gaba da kiyaye zaman lafiya a kasar ta Mali.
A daren ranar 31 ga watan jiya ne aka kai harin ta'addanci har sau biyu, a sansanonin rundunar MINUSMA, inda mutane 4 suka rasa rayukansu, ciki had da wani Basine daya, yayin da wasu fiye da 10 suka jikkata. (Tasallah Yuan)