Ministan aikin gona da raya yankunan karkara na Najeriya Audu Ogbeh ne ya bayyana hakan Abuja, fadar mulkin kasar lokacin da yake jawabi a bikin kaddamar da wani shirin hadin gwiwa na dala miliyan biyu tsakanin gwamnati da bangaren sassa masu zaman kansu kan yadda za a inganta bangaren noman kasar.
Minista Ogbeh ya kuma bayyana cewa, gwammatin tana shirin samarwa manoma da masu zuba jari a sashen noman kasar masu kula da lafiyarsu, a wani mataki na karfafawa manoman gwiwa zama a cikin gonakansu, sabanin yadda aka saba gani a sauran sassan duniya, inda manoma ke zaune a cikin gonakansu.
Ogbeh ya ce gwamnatin na shirin kawo karshen kai komo da Fulani makiyaya suke yi daga wannan wuri zuwa wancan don neman abinci dabbobinsu. (Ibrahim)