Rukunin bada kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa na rundunar sojojin ruwan kasar Sin na 22 ya kammala ziyararsa ta kwanaki hudu a ranar Jumma'a a kasar Afrika ta Kudu.
Rukunin dake kunshe da na'urar harbe rokoki, jiragen sama na yaki, da jirgin ruwan yaki na jigilar kayayyaki, ya bar sansanin sojojin ruwan Afrika ta Kudu dake Simon's Town mai tazarar kilomita 30 dake kudancin Cap a ranar Jumma'a da safe, bayan wani bikin da ya samu halartar jakadan Sin daka kasar Afrika ta Kudu Tian Xuejun, wakilan rundunar sojojin ruwan Afrika ta Kudu da kuma 'yan kasar Sin dake zama a Afrika ta Kudu.
Ziyarar wannan rukuni ya biyo bayan karshen aikin tawagar bada kariya a yankin tekun Aden da kuma yankin ruwan Somaliya da aka fara a cikin watan Disamban shekarar 2015 zuwa watan Afrilun shekarar 2016.
A yayin wannan rangadi, rukunin rundunar sojojin ruwan Sin ya gudanar da atisayen soja tare da rundunonin ruwan Afrika ta Kudu da zummar karfafa musanya da dangantaka tsakanin rundunonin ruwan kasashen biyu. Haka kuma ranakun bude kofa ga jama'a sun taimakawa mutane kai ziyara ga rundunonin ruwan kasar Sin.
Wannan shi ne karo na hudu da rundunar sojojin ruwan Sin ta kai ziyara a Afrika ta Kudu. Tare da iznin MDD, rundunar sojojin ruwan Sin na tura tun daga shekarar 2008 jiragen ruwan yaki a yankin tekun Aden da yankin ruwan Somaliya domin bada kariya ga jiragen ruwan dakon kaya daga hare haren 'yan fashin teku. (Maman Ada)