Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a garin Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin, yayin da ya kai ziyara aiki ta yini guda a jihar. Ya kuma bayyana cewa, al'amuran tsaro za su ci gaba da inganta a lokacin shugabancinsa.
Ya ce, ya ziyarci jihar Zamfara ce, domin ya karfafawa sojojin gwiwa a lokacin da ake bikin ranar sojojin kasar ta shekarar 2016. Kuma taken bikin na bana shi ne kawar da masu satar shanu da 'yan fashi a jihar da sauran jihohi kamar Kaduna, Kebbi, Katsina da kuma Sokoto.
Shugaban Najeriyar ya kuma ba da tabbacin cewa, nan ba da dadewa ba za a farfado da bangaren tattalin arzikin kasar, ta hanyar sabbin manufofin raya tattalin arziki da na kudi da babban bankin kasar ya bullo da su. (Ibrahim)