in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
M.D.D. ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. a Mali
2016-06-02 10:20:52 cri
A jiya Laraba ne, kwamitin sulhu na M.D.D. da sakatare janar na majalisar Ban Ki-Moon suka ba da sanarwa, inda suka yi Allah-wadai da harin ta'addanci da aka kai wa sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke kasar Mali wato MINUSMA, tare da janjantawa dangin sojan kiyaye zaman lafiya na Sin da ya rasu da kuma gwamnatin Sin.

Kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi kira ga gwamnatin Mali da ta hanzarta gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Kwamitin sulhu na M.D.D. ya jaddada cewa, bisa dokokin kasa da kasa, harin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya tamkar laifin yaki ne. A cikin sanarwar da kwamitin sulhu na M.D.D. ya bayar, an sake nanata bukatar yaki da ayyukan ta'addanci.

A yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana, kakakin sakatare janar na M.D.D. StephaneDujarric ya karanta sanarwar Mr. Ban, inda ya bayyana cewa, M.D.D. za ta ci gaba da nuna goyon baya game da kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Mali. A kwanakin nan ne, Ban Ki-Moon zai gabatar da shawarwari game da inganta kwarewar sojojin MINUSMA.

Tuni, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying ta ce, harin ta'addancin da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. babban laifi ne, bai kamata a kyale shi ba. Sin ta yi tofin Allah tsine game da wannan batu da kakkausar murya. Sin ta bukaci gwamnatin Mali da M.D.D. da su gudanar da bincike game da lamarin, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kuliya, sannan a taimakawa kasar Sin wajen daidaita batun mutuwar sojin kasar.

A ranar Talata da dare ne, aka kai hari kan sansanin sojojin MINUSMA da ke garin Gao, harin da ya haddasa mutuwar wani sojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, tare da jikkatar wasu 4. Yanzu haka an garzaya da sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin guda 2 zuwa asibitin dake cibiyar birnin Dakar hedkwatar kasar Senegal, don yi musu jinya.

A jiya Laraba ne, reshen kungiyar Al-Qaeda dake yankin arewacin kasashen Afrika wato Magreb ya sanar da daukar alhakin kai wannan hari.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China