Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da daraktar hukumar lafiya ta duniya shiyyar Afrika Dr. Matshidiso Rebecca Moeti a Abuja, fadar gwamnatin kasar.
Yace akwai bukatar hukumomin lafiya na kasa da kasa su tabbatarwa Najeriyar matsayinta na yin bankwana da cutar poliyon.
Buhari ya ce, shekaru biyu kenan da suka gabata ba'a samu rahoton bullar cutar ba, koda yake batun rikita rikitar da ake samu game da rashin bin dokokin alluran rigakafin a shiyyar arewa maso gabashin kasar, ya kasance a matsayin wata babbar barazana ga batun na rigakafi.
Shugaban Najeriyar ya ce halin da yara kanana ke ciki a sansanonin yan gudun hijira dake kasar abin tausayi ne.
Ya kara da cewar, gwamantinsa zata cigaba da bada fifiko ga fannin kiwon lafiya ta hanyar ware kudaden gudanar da shirye shiryen da suka shafi kiwon lafiya.
Tunda farko, Moeti ta yabawa shirye shiryen kiwon lafiya na kasar, kana ta yi alkawarin cewa hukumar ta WHO zata cigaba da taimakawa fannin lafiya a kasar.(Ahmad Fagam)