Mai Magana da yawun hukumar 'yan sandan Najeriya Don Awunah ya shedawa manema labaru a Abuja cewar, an damke mutanen da ake zargin ne ta hanyar wasu dabaru da 'yan sanda kasar suka tsara.
An yi garkuwa da janar Claude-Nelson ne a ranar 30 ga wata Yuni a lokacin da yake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma masu garkuwar, sun sake shi ne a ranar 5 ga wannan wata na Yuli.
Kakakin 'yan sandan ya ce tawagar binciken sirri ta hukumar ce ta damke mutanen 11 da ake zargi da cin karensu ba babbaka a shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.
Awunah ya ce, daya daga cikin dabarun da bata garin ke amfani da su shi ne, datse manyan tituna da kuma sa kayan sarki don badda kama inda suke kaddamar da hare hare kan masu zirga zirga a kan titunan.
Jam'in ya tabbatarwa jami'an diplomasiyya dake Najeriya cewar, za'a samar musu da isasshen tsaro a kasar, kana za'a gurfanar da wadanda ake zargin a kotun bayan kammala bincike.(Ahmad Fagam)