in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 800 suna ci gaba da fama da kangin talauci a duniya
2016-07-19 20:21:28 cri
An gabatar da rahoton neman samun ci gaba da bunkasar kasashen duniya baki daya, a gun taron cinikayya da bunkasuwa na MDD karo na 14 da ya gudana a jiya Litinin a birnin Nairobin kasar Kenya.

Rahoton dai ya bayyana cewa, a cikin shekarun baya bayan nan, ko da yake an samu sakamako mai kyau a fannin rage yawan matalauta, musamman ma ganin yadda kasashen Sin da India suka nuna kwarewa matuka wajen yaki da kangin talauci, sai dai duk da hakan akwai mutanen da yawan su ya kai miliyan 836 da ke fama da kangin talauci a sassan duniya baki daya.

Rahoton ya kara da cewa, duk da cewar yawan matalauta ya ragu a duniya, a daya hannun akwai tazara sosai a tsakanin kasashe daban daban a fannin kubutar da jama'ar su daga kangin talauci. Ya ce a halin yanzu, galibin mutanen da suka fi fama da talauci na zaune ne a kasashen dake kudu da hamadar Sahara, da kuma yammacin Asiya.

A game da matsalolin da kasashen Afrika suke fama da su a fannin neman samun bunkasuwa kuwa, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya bayyana a gun taron cewa, kasashen Afrika suna da karancin tsari mai inganci na gudanar da harkokinsu a fili. Don haka ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD da su kara yin hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen Afrika, wajen lallubo hanyoyin warware matsalolin nahiyar yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China