Mr. Wang ya ce daukar wannan mataki na da nasaba da burin samun rayuwa da bunkasuwar jama'a mai inganci a kasashen duniya, idan aka yi la'akari da burin kasashe masu tasowa na raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar su.
Wang Min ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar, yayin muhawarar da ta gudana a taron koli, na majalisar kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta MDD na shekarar 2015 a jiya Laraba.
Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su dora muhimmanci game da kudurin kawar da talauci, da sa kaimi ga samun bunkasuwa, hakan, a cewarsa zai taimaka a tinkari sabbin kalubalen dake shafar rashin ci gaban tattalin arziki cikin sauri, da tsaron makamashi, da sauyin yanayi da dai sauransu. (Zainab)