Taken taron shi ne, 'samun hakki na daidaituwa nan take'. An sanya wannan taken ne don nuna muhimmancin samar da isashen kudi don hana yaduwar cutar da kuma nazarinta, da jinyar wadanda suka kamu da cutar, da masu dauke da kwayoyin cutar cikin sauri, da daina nuna bambanci ga 'yan luwadi, da masu shan miyagun kwayoyi, da masu aikata karuwanci.
Mutane kimanin dubu 18 da suka hada da manyan jami'ai, da masana, da wakilan masu dauke da cutar kanjamau sun halarci taron.(Bello Wang)