in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kafa jami'ar koyon fasahohin sadarwa ta farko ta Afirka a kasar Nijeriya
2016-07-19 10:45:28 cri
Jaridar THIS DAY da ake wallafawa a Nijeriya ta bayar da wani rahoto a jiya Litinin cewa, ministan harkokin sadarwa na kasar Adebayo Shittu ya bayyanawa 'yan jarida cewa, gwamnatin kasar tana shirin kafa jami'ar koyon fasahohin sadarwa ta nahiyar Afirka ta farko a Nijeriya don horar da kwararru a wannan fanni. Shittu ya bayyana cewa, wannan wani bangare ne na shirin raya fasahohin sadarwa da kasar Nijeriya ta bullo da shi, wanda za a gabatar da shi nan da wasu 'yan makwanni masu zuwa. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China