in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu dakaru sun yi garkuwa da mutane 5 a kasar Nijeriya
2016-06-23 11:47:22 cri
A jiya Laraba 22 ga wata, wasu dakaru sun yi garkuwa da mutane 5, ciki har da 'yan kasashen waje 3 a yankin Akpabuyo dake jihar Cross River a kudu maso gabashin kasar Nijeriya.

Shugaban 'yan sandan jihar Jimoh Ozi-Obeh ya bayyanawa 'yan jaridan kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, yanzu 'yan sanda suna hadin gwiwa tare da sojojin ruwan kasar don tabbatar da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Jami'in ya bayyana cewa, mutanen 5 da aka yi garkuwa da su sun hada da 'yan kasar Australia 2, dan kasar Afirka ta Kudu daya da kuma 'yan kasar Nijeriya biyu. Kana ya ce, an harba matukin motar da suke ciki har lahira.

Lamarin ya faru a ranar jiya Laraba da karfe 7 na safe a kan gadar Edundun. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China